1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tattalin arziki a Zimbabuwe

Gazali Abdou Tasawa
January 14, 2019

Gwamnatin Shugaba Emmerson Mnangagwa a Zimbabuwe ta kara farashin kudin man fetur a kasar a wani mataki na shawo kan matsalar tattalin arziki da kasa ta fada a ciki. Sai dai matakin ya bar baya da kura.

https://p.dw.com/p/3BX65
Simbabwe Präsidentschaftswahl Emmerson Mnangagwa erklärter Wahlsieger
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Tuni dai matakin gwamnatin ta Zimbabuwe ya haifar da martani daga bangarorin al'uma dabam-dabam na kasar. Wasu na korafi kan yadda bayan karin farashin man aka wayi gari ba a samunsa a gidajen man fetur na kasar. Lamarin da ya soma kawo cikas ga harakokin zirga-zirga a kasar. Daga nasu bangaren masu motocin sufuri na dora ayar tambaya kan kudaden da ya kamata su karba kan fasinjoji bayan karin kudin man.

Wirtschaftskrise in Simbabwe
Hoto: picture alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

Suma dai ma'aikatan gwamnatin kasar sun fusata inda suka bayyana bukatar karin albashi ta hanyar amfanin da Dalar Amirka domin samun kariya daga matsalolin tattalin arziki. Daruruwan likitoci suna yajin aiki fiye da wata guda. Yanzu malaman makaranta suna barazanar shiga yajin aiki na kasa baki daya cikin kwanaki masu zuwa.

Gwamnati ta bukaci a kara hakuri. Shugabannin siyasa sun ce za a shawo kan matsalar ta hanyar tsuke bakin aljihu. Shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar ta Zimbabuwe ya yi gargadi ga wadanda ya zarga da ke neman amfani da wannan dama domin zagon kasa ga gwamnati. Gwamnati ta ce tana sake duba matakan kyautata wa ma'aikata har zuwa lokacin da za a sake duba tsarin albashi cikin watan Afrilu mai zuwa na wannan shekara ta 2019 kamar yadda yake a cikin tsarin kasafin kudi.

Simbabwe Amtseinführung des neuen Präsidenten Emmerson Mnangagwa
Hoto: DW/Ralph Chikambi

Tuni kungoyin kwadago suka yi fatali da zancen na gwamnati abin da suka kira a matsayin yaudara. A makon jiya gwamnatin ta yi tayin kara kashi 10 cikin 100 na albashi daga watan Afrilu, amma kungiyoyin sun yi fatali da haka, inda suka ce gwamnatin da ke rayuwa ta kasaita da facaka, sannan tana shaida wa ma'aikata su daura damara.

Rikicin tattalin arziki na zama babban kalubale da ke gaban sabuwar gwamnatin Zimbabuwe tun bayan kawo karshen mulkin tsohon Shugaba Robert Mugabe wanda ya dade kan madafun iko, tun lokacin an samu tashin farashin kayayyaki da suka nunka kimanin sau uku, ga karancin man fetur inda masu ababen hawa ke kwashe tsawon kwanaki a layukan gidajen man fetur.