1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korafe-korafe kan kudin beli da 'yan sanda ke karba

Nasir Salisu Zango MAB
September 27, 2019

Sau da dama 'yan sandan Najeriya na shiga rikici da al'umma bisa zargin amfani da kakinsu wajen karbar kudade beli daga hannun iyalan wanda aka tsare, lamarin da ke haddasa zaman doya da manja tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/3QMzx
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture alliance/NurPhoto

 

A jihar Kano dai galiban harabar chaji ofis din 'yan sanda na cike da rubuce-rubuce da harshen Turanci da Hausa wanda ke cewar beli kyauta ne, amma sannu a hankali wannan ya tasamma zama tamkar wani zane da ake kawata harabar chaji ofis da shi, musamman ta la'akari da cewar wasu daga ciki sun zama tamkar kasuwar kaji ko agwagi. Ana kama mutum a saka shi a akurki a rufe kafin 'yan uwansu su zo ayi ciniki kuma su biya kudin fansar 'yan uwansu.

Muhammad Bala guda ne daga cikin wadanda aka kama wa dan uwa a kan laifin da bai shafi 'yan sanda ba, ya bayyana cewar babban abin da yake ba su mamaki shi ne yadda da ka shiga chaji ofis za a fara ciniki kuma hannu da hannu ka mika kudin beli. Shi ma Abubakar Ibrahim magidanci wanda ya ce ya je belin wani sabon ango amma aka sanya kudin beli mai tsada, lamarin da ya sa a dole aka yi Karin Naira dubu daya da dari biyar. Sai da angon ya yi honeymoon din kwana guda a gadirun din 'yan sanda tukuna sakamakon rashin cikon balas din beli. 

Nigeria Polizei
Rundunar 'yan sanda ta ce mai karba da mai bayar da beli na da laifiHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce mai karba da me bayar da belin suna da laifi, amma suna kokarin farautar 'yan sanda da ke karbar kudin beli domin hukuntasu. Amma masana a fannin shari'a irinsu Barista Abba Hikima na ganin baiken rundunar 'yan sanda bisa yadda ake wakaci ka tashi da shiga shara ba shanu wajen shiga batutuwna da ba su sha fe su ba. Yanzu haka dai jikin mutane ya fara sanyi dangane da baitukan bail is free wanda ke ci gaba da haddasa kallon hadarin kaji tsakanin 'yan sanda da al'ummar gari.