Komitin sulhu yana ci gaba da tattunawa akan Iran | Labarai | DW | 29.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu yana ci gaba da tattunawa akan Iran

Komitin sulhu na MDD yana ci gaba da taronsa a kokarin samo yarjejejniya ta bai daya ta yadda zaa bullowa shirin nukiliya na kasar Iran kafin taron ministocin harkokin wajen komitin kasa da saoi 24 masu zuwa.

Burtaniya da Faransa dai sun mika shawarrinsu ga taron a jiya talata,inda suka sassauto game da bukatun Rasha da SIN,wadanda suke ganin cewa,duk wani mataki da aka dauka wani shiri ne na lakabawa Iran takunkumi ne anan gaba.

Jakadan kasar Sin a taron ya fadawa manema labarai cewa,gwamnatin kasar Sin bata gamsu da abinda shawarwarin suka kunsa ba,muddin dai an samu amincewar zaunannun membobi 5 na komitin ciki har da SIn da Rasha akwai yiwuwar sauran membobi zasu amince da duk shawara da aka yanke.