Komitin sulhu ya kasa cimma matsaya akan Iran | Labarai | DW | 08.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu ya kasa cimma matsaya akan Iran

default

Wakilan kasashe 5 na dindindin na komitin sulhu sun sake ganawa a yau game da batun nukiliya na kasar Iran,ba tare da samun wani ci gaba mai maana ba,kafin taron ministocin kasashen game da batun a brinin New York.

Wakilan kasashen Amurka,Sin,Burtaniya,Rasha da Faransa sun gana a asirce na tsawon mintuna 30,amma sun gagara kawadda kiki kaka dake tsakaninsu game da shawarwarin da Burtaniya da Faransa suka bayar wanda zai tilsatawa Iran bisa sharia ta dakatar da shirinta na nukiliya.

Har yanzu dai kasashen Rasha da Sin suna kan bakarsu ta kin amincewa da lakaba takunkumi ko yin anfani da karfin soji wajen tilasatwa Iran din ta dakatar da inganta sinadaren uranium.

Nan gaba a yau ne kuma sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice zata karbi bakuncin takawrorinta na manyan kasashen duniya 5 wajen liyafar cin abincin dare,inda zasu ci gaba da tattaunawa da nufin kawo karshen banbance banbance dake tsakaninsu game da mataki daya kamata su dauka akan kasar ta Iran.