Komitin sulhu ya amince da aika dakarun AU zuwa Somalia | Labarai | DW | 07.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin sulhu ya amince da aika dakarun AU zuwa Somalia

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bada umurnin kafa wata rundunar Afrika da zata kare gwamnatin kasar Somalia daga barazana da take fuskanta daga dakarun kotunan islama a da suke da karfi a kasar.

Kudirin wanda kasashen Afrika membobi suka bukaci a bullo da shi,ya kuma dage takunkumin makamai daga Somalia domin baiwa dakaraun Afrikan damara samun makamai da kayan aikin soji da zasu horasda jamian tsaron gwamnati.

A waje guda kuma,yayi barazanar dora takunkumi akan wasu bangarori da zasu iya a karya dokokin takunkumin haramta sayarda makaman.

Hakazalika kudirin ya bukaci mayakan kotunan musulunci da su dakatar kame garuruwa da sukeyi su kuma tattauna da gwamnatin wucin gadi tare da nufin tsagaita bude wuta da kwanciyar hankali na siyasa a kasar.