Kokarin yin sulhu a rikicin Yemen | Siyasa | DW | 20.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin yin sulhu a rikicin Yemen

Bayan da a wannan Litinin din 19 ga watan Janairu 2015 mayakan Houthi suka yi kawanya ga gidan Firaministan Yemen a birnin Sana'a, shugaban kasar ya nemi a yi sulhu.

Ministar yada labaran kasar Nadia Sakaff ta ce shugaba Abd Rabu Mansour Hadi a safiyar wannan Talata ya kira jagororin siyasar kasar ciki kuwa harda 'yan Houthi dan lalubo mafita ga matsalar da kasar ta samu kanta na rashin tabbas. Wannan tattaunawa dai na zuwa ne bayan da 'yan awaren na Houthi suka ajiye motocinsu a shingayen bincike dauke da manyan bindigogi na harbo jiragen yaki a cikin birnin na Sana'a kusa da gidan Firaminista yayin da sauran sojojinsu ke kai kawo a tinunan na birnin.

Tattaunawa domin nemo mafita

A cewar mai magana da yawun shugaban kasar Rageh Badi shugaba Abed Rabbo Mansour Hadi da mai bada shawara ga bangaren na Houthi na tattaunawa kan wasu muhuimman batutuwa da zasu fitar da makomar kasar da ta shiga rudani tun daga watan Satumbar bara. Ministar yada labarai Nadia Sakaff ta ce a fafatawar da aka yi jiya mutane takwas ne suka rasa rayukansu yayin da 32 suka samu raunuka. Sai dai a cewar Elias Manea da ke aikin agaji kuma ke sintiri da motar daukar marasa lafiya har yanzu basu da cikakken bayani kan wannan adadi.

Tun da fari ministan lafiya na kasar ta Yemen Yassin Abdullah ya bayyana cewa mutane 55 ne ake basu kulawa a asibiti. Wannan dai na nuna rashin cikakkiyar masananiya kan wadanda abin ya ritsa da su daga bangaren mahukuntan da suma ba su da ta cewa, amma a cewar Elias Manea da suke wannan aiki na ceto rashin samun bayanan nada nasaba kan rashin isar jami'an agaji inda aka fafata.

Ci gaba da jan daga

A gaban fadar shugaban kasar mayakan na Houthi sun ja daga da tazarar kimanin mita 500 daga kofar shiga fadar shugaban kamar yadda wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya bayyana. A Wani abu da ke nuna irin munin barazana da wannan gwamnati da ke samun goyon bayan Amirka ke fuskanta, inda rahotanni ke nuni da cewar an ma kai farmaki kan motar ofishin jakadancin Amirka a birnin na Sana'a. Mayakan na Houthi dai a wannan karo sun matsa lamba a fadar gwamnatin kasar ta Sana'a, inda baya ga kwace sansanin sojoji da kafar yada labaran gwamnati abu na gaba da ake ganin na iya zama abin da suke son kaiwa gareshi shine fadar shugaban kasar ta Yemen inda anan ma dakarun sojoji cikin damara ke cikin shirin ko ta kwana