Mali: Sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu
May 15, 2015Talla
Sai dai babbar kungiyar hadaka ta 'yan tawayen kasar "The Coordination of Azawad Movements" (CMA) da ke fafutukar ganin samun 'yancin kan yankin Abzinawa ta sanar da cewa ba za ta halarci bikin na Bamako babban birnin kasar ta Mali ba. Tuni dai shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe wanda kuma shine shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU ya isa birnin na Bamako yayin da ake sa ran halartar akallah shugabannin kasashen nahiyar Afirkan 20 wajen wannan biki. Bikin dai ya biyo bayan kwashe tsahon watanni da Majalisar Dinkin Duniya ta yi tana shiga tsakani domin tabbatar da ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Mali.