1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: Samar da sabuwar ranar zabe

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 23, 2021

'Yan majalisun dokokin Libiya na shirin yin wata ganawa domin tattaunan batun sabon lokacin gudanar da zabe a kasar, bayan da aka dage zaben shugaban kasa da a baya aka shirya gudanarwa a wannan makon.

https://p.dw.com/p/44muu
Libyen Premierminister Abdul Hamid Mohammed
Firaministan Libiya Abdul Hamid Mohammed DbeibahHoto: Hazem Ahmed/AP Photo/picture alliance

Majalisar wakilan kasar ta ayyana cewa ba za a iya gudanar da zaben da aka shirya gudanarwa domin kawo karshen rikicin kasar na tsawon shekaru ba, inda ta ce tilas a sake daukar lokaci. Wani dan majalisar wakilan da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an nada kwamiti da zai tattauna batun sanya sabuwar ranar gudanar da zaben. Hukumar zaben kassar dai ta bayar da ashawwarar a dage zaben har zuwa ranar 24 ga watan Janairun shekara mai zuwa ta 2022, sai dai ganin yadda ake cikin takun saka tsakanin majalisar dokoki da ke gabashin kasar da kuma gwamnati a Tripoli amincewa da ranar gudanar da zaben zai yi wuya.