1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Italiya ta ba da hanyoyin warware yakin Ukraine

May 20, 2022

Italiya ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya shawara kafa wani kwamiti na masu shiga tsakani na kasa da kasa a kokarin cimma matsaya ta kai wa ga matakin tsagaita wuta a yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha.

https://p.dw.com/p/4BepW
Türkei Istanbul | Verhandlungen zwischen Russland und Ukraine
Hoto: Turkish Presidency/AP/dpa/picture alliance

Shirin na Italiya ya zo ne a daidai lokacin da rikicin kasar ta Ukraine ke kara tabarbarewa, wanda ke yin barazanar kara ta'azzarar matsalolin makamashi da na abinci a duniya baki daya. Yayin da yake matukar kawo cikas ga ayyukan noma da fitar da cimmaka daga kasar Ukraine, zuwa kasashen waje. Kasar ta Ukraine dai ta kasance ta hudu a duniya wajen noman masara kana ta uku wajen noman alkama.