Kokarin samar da zaman lafiya a Libiya | Labarai | DW | 22.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin samar da zaman lafiya a Libiya

Wakilai na 'yan majalisun dokoki na Libiya na bangarori biyu da ke rikici kan iko sun soma yin wani sabon zagaye na tattaunawa a Maroko domin samun daidaito tsakanin sasan biyu.

Taron wanda ake yi Bouznika a kudancin Maroko ya hada 'yan majalisun dokokin na Tabruk wanda ke a karkashin ikon janar Haftar  da kuma wandanda ke yin biyaya ga gwamnatin wucin gadi da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Kasar Libiya ta fada cikin wani hali na rishin tsayayyar gwamnati tun bayan faduwar gwamnatin Muammar Kadhafi a shekara ta 2011.