Kokarin neman mafita kan rikicin kasar Burundi | Labarai | DW | 14.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin neman mafita kan rikicin kasar Burundi

A yayin da mako guda ya rage a kai ga zaben shugaban kasa a Burundi, Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya soma jagorantar wata tattaunawa mai sakakiyar gaske.

Wannan aiki na shugaba Museveni da kungiyar EAC ta kasashen gabashin Afirka ta dora masa bayan rishin samun nasara a tattaunawar da aka yi a baya, na zaman mai wahalar gaske ganin yadda bengarorin kowa ya kife kan bakansa. A cewar Léonce Ngendakumana, daya daga cikin kusoshin adawar kasar ta Burundi, suna jiran abubuwa da dama daga Shugaba Museveni, ba wai a matsayinsa na mai shiga tskani ba kawai, a matsayinsa na mai kare yarjejeniya birnin Arusha wanda yake daya daga cikin wadanda suka kirkirota.