Kokarin kawar da rikicin siyasar Yemen | Labarai | DW | 13.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kawar da rikicin siyasar Yemen

A wani yunkuri na kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Yemen, shugaban kasar ya sanar da nadin Khaled Bahah a matsayin firaministan kasar.

Jemen Plakat Präsident Mansour Hadi

Shugaban Yemen Abd Rabbuh Mansur Hadi

Wata majiya daga fadar shugaban kasar ta ce Bahah na daga cikin mutane ukun da 'yan Houthi da ke bin tafarkin Shi'a a kasar suka bada don zabar guda daga cikinsu da za a nada a wannan matsayi, bayan da suka yi watsi da nadin Ahmed Awad Bin Mubarak da aka yi a makon jiya.

Masu sanya idanu kan rikicin siyasar kasar na ganin wanann nadi da aka yi zai taimaka wajen kawo karshen tada jijiyar wuyan da 'yan kungiyar ta Houthi ke yi a kasar wanda a watan jiya suka kame Sanaa babban birnin kasar.