Kokarin karbe makamai a Burundi | Siyasa | DW | 09.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin karbe makamai a Burundi

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa domin tattauna halin da ake ciki a kasar Burundi.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza

A daidai lokacin da kwamitin sulhun ke shirin gudanar da taron kan Burundi, gwamnati ta kaddamar da shirin kwance damarar wadanda ke dauke da makamai. Matakin gwamnatin dai ya biyo bayan cikar wa'adin da gwamnatin ta bawa masu rike da makaman na su mika su bisa radin kansu tun a makon jiya. Tuni mutane biyu suka rasa rayukansu sakamakon matakin da gwamnatin ta dauka na karbe makaman. Unguwar Untakora da ke Bujumbura babban birnin kasar nan ne wuri na farko da sojojin da ke kwance damarar mayakan suka fara isa. Ministan tsaron kasar janar Alain Gillaume Buyoni shi ne ya kaddamar da shirin yana mai cewa:

Maboyar masu rike da makamai

"Nan inda muke wuri ne da wadanda suke dauke da makamai suka saba zama wanda kuma daga nan sukan jefa gurneti, da abubuwa masu fashewa a kan jama, banda nan ma a wurare da dama haka na faruwa. Muna jan hankalin jama'a cewa komai na tafiya yadda ya kamata kuma muna bukatar hadin kansu."

Kokarin raba mutane da makamai a Burundi

Kokarin raba mutane da makamai a Burundi

Kusan kwanaki hudu kenan da mutane da dama suka fice daga gidajensu a wasu unguwanni da ke birnin na Bujumbura inda sojojin suka yi wa kawanya kana kuma harkokin zirga zirga sun tsaya cak. Mutanen dai na kauracewa unguwanin Mutakura da Ciboteke inda ake gudanar da binciken domin neman masu dauke da makamai, tare da tserewa zuwa wasu unguwanin.

Tursasawar jami'an tsaro

Wannan na daga cikin wadanda ke kokarin yin kaura saboda abin da ya kira tursasawa da jamian tsaron ke yi wajen gudanar da binciken karbe makaman. Ya kara da cewa:

"Indai har mutum ya yanke shawarar daukar makami, to ya yi ammanna cewa rayuwarsa na fuskantar hadari ne saboda rashin tsaro, ya zama dole kuma wajibi gwamnati ta kula da taron al'umma saboda kada mutane su dauki makami domin kare kansu."

Al'ummar wasu unguwanni a Burundi na yin kaura

Al'ummar wasu unguwanni a Burundi na yin kaura

Akalla mutane biyu 'yan sanda suka harbe a cikin unguwanin yayin da wasu suka jikkata a ciki har da wani dalibi. Wani babban jam'in 'yan sanda wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce da farko mutanen unguwar ne suka jefa wa 'yan sandan da ke yin sintiri a unguwar gurneti a lokacin da motarsu ke wucewa kafin 'yan sandan su mayar da martani, Severine wata saidar gani da ido ce ta kuma ce:

"Mun gaji da ganin gawarakin mutane, nan da can mun wahala mun rasa 'yan uwa, muna yin kira ga 'yan sanda da su daina kashe mutane mu zaman lafiya muke so."

Tashin hankalin kasar ta Burundi dai ya biyo bayan takarar shugaba Pierre Nkurunzaza wanda ya yi tazarce a wa'adi na uku duk kuwa da cewar hakan ya saba wa dokokin kasar. Ya zuwa yanzu hargitsin ya janyo mutuwar mutane sama da 200 yayin da wasu 20,000 suka kauracewa matsugunasu. Sai dai ta yi wu kwamitin sulhu na Majalisar Ddinkin Duniya ya yi kokarin daukar muhimman matakai dangane da halin da ake ciki a Burundi a karshen taron musamman da kwamitin ke yi kan Burundin.

Sauti da bidiyo akan labarin