Kokarin ingata tsaro a tekunan Afirka | Siyasa | DW | 12.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin ingata tsaro a tekunan Afirka

Kungiyar Tarayyar Afirka na shirin tunkarar matsaloli da ake fiskanta kan tekunanta kama daga masu fashi da kuma kamun kifi gami da magance karuwar gurbacewar ruwayen kasashen

A karshen mako ne dai kwarru kan harkar ruwaye, dana tsaro daga kasashen na Afirka za hallara a Lome, babban birnin kasar Togo, domin yin bita kan wadannan matsaloli. A cewar ministan harkokin wajen kasar Togo Robert Dussey, fashin teku kama daga tekun Aden wande ke gabar ruwayen Somaliya, izuwa tekun Gini da ya ratsa kasashen yammaci da tsakiyar Afirka, a shekrun baya-bayannan sun kasance wata babbar barazana ga sufurin jiragen ruwa, inda kama daga shekara ta 2005 izuwa yanzu, aka yi kiyasin an kai farmaki a tsakanin wadannan tekuna har sama da 205.

 Robert Dussey, ya kara da cewa daga cikin 54 da ke kungiyar Tarayyar Afirka, kasashe 33 cikin su, suna iyaka ne da gabar teku, don haka kula da tsaron teku babbar bukata ce ga duklkan kasashen kungiyar, inda yace kimanin kashi 92 cikin dari na kayakin da ake shigowa da su kasashen Afirka, anan shigo da su ne ta ruwayen teku.

Ci-gaba a Najeriya

 Bisa dai kokarin jami'an tsaro da ke farautar 'yan fashin kan Teku, zaa iya cewar an dan sami saukin lamarin kan teku a Najeriya, in aka kwatanta da musamman bayanan da cibiyar kula da tsaran zirga-zirgar jiragen ruwa ta kasa da kasa, ke bayarwa kan Najeriyar a baya. To sai dai masu  zirga-zirga a tsakankanin garuruwan alummomi ta ruwa a yankin Niger Delta, na batun har yanzu akwai dar-dar din kananan 'yan fashin kan ruwa. A cewar wakilin DW a 'yankin Niger Delta Muhammad Bello, lafawar kokawar musamman cibiyar IMB da ke sa'ido kan tsaron jiragen ruwan  na kasa da kasa, kan yawaitar 'yan fashin teku a ruwayen Najeriya ,shi ne ya nuna alamun raguwar ta'annatin 'yan fashin kan teku a Najeriyar. Bugu da kari ga dukkanin alamu, rundunar tsaron sojoji, musamman na ruwa ta kasar ta daura damarar yaki da 'yan fashin teku, inda ma bayanai suka tabbatar suna ta aikin sintiri na tsaro tsakanin manya da kananan ruwaye a yankin na Niger Delta.

MS Taipan Piraten Somalia (AP)

'Yan fashi kan teku dai a Najeriyar saida suka haifar da matikar damuwa a kafatanin ruwayen teku Gini. Kelvin Dikibo wani dan asalin yakuna da aka fi yin fashin teku a gabar ruwayen Najeriy a yankin Niger Delta, yace dakarun tsaron Najeriyar sun yi aiki sosai, koda yake da dan sauran rina a kaba. Kelvin Dikibo ya kara da cewar gwamnatin Najeriya na kokari sosai wajen tura jamian tsaro don samar da tsaron zirga-zirga ta ruwa, sai dai kuma fa har yanzu 'yan fashin kan teku na nan, na kulle kucirya da jamian tsaro. A dalilin cewar 'an fashin sun san hanyoyi na badda sawu a kan ruwayen, kuma 'yan fashin kan afkama mata, bayan sun amshe abubuwan duk da ke hannunsu, wani lokacin su umarci fasinjojin jirgi maza cewar, dole sai sun yi lalata mata dake jikin jirgin ruwan.

A Najeryar 'yan fashin kan ruwa dai a musamman kan fara daga kananan ruwaye, kafin tsallakawa kan teku. An tabbatar cewar 'yan ta'annancin da ke bangaren ruwayen Najeriya sun fi muni matika, inda bayan afkawa man'yan jiragen kasas da kasa, sukan kama matuka jiragen, ta inda sai sun karbi kudaden fansa kafin sakinsu, bayan sace kafatanin ababen amfani daga cikin jirgin duk da suka afkawa, koma wani sailin su karkata akalar jirgin zuwa wani boyayyen sansani nasu. Alkaluma dai sun tabbatar da cewar, rayukan da suka salwanta ba kadan bane na ma'aikatan jiragen ruwa ko fasinjojinsu a wasu lokutan idan aka bude wuta kan jiragen.
Wani Mr Sotonye Jamaica dan yankin tsibirin Bonny ne a jihar Rivers, da zuwan garin nasu na Bonny kan dau kimanin awa daya ta kan ruwa, kuma a bayaninsa lamarin na 'yan fashin kan teku na bukatar namijin kokari daga hukumomi.

Ya ce "Yan fashi kan Teku sun dada tsanata fa, domin a kwanananne ma, basaraken shiyyar mu ya kira taron jami'an tsaro da dukkanin masu ruwa da tsaki kan tsaro kan ruwa, inda kuma aka tattauna matsalar tare da daukar mataki. Kwanannan ne ma dai 'yan fashi suka farma wasu mata, matafiya inda suka yi lalata dasu, lamarin da ya tada hankalin jama'a".

Duk da dai nasarori da ake ganin cewar dakarun tsaro sun samu kan dakile barazanar 'yan fashin na kan teku a ruwayen Najeriyar, akwai bukatar tsananta tsaro kan kananan ruwaye, inda daga nanne 'yan fashin teku kan koyi harkar, kuma su zarce da yin fashi a manyan ruwaye, don addabar jiragen kasa da kasa.