Kokarin gano mahara a Kenya | Labarai | DW | 15.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin gano mahara a Kenya

Hukumomin Kenya na farautar maharan da suka yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane shida a kasar.

'Yan sandan kasar Kenya sun kaddamar da binciken hari kan motar safa da ya yi sanadiyar hallaka mutane shida, yayin da wasu 30 suka samu raunika. Kuma hari na baya-baya cikin bukukuwan cika shekaru 50 da samun 'yanci da aka gudanar a kasar.

Wasu rahotannin sun ce an yi amfani da gurneti wajen kai harin, kuma kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin wannan hari.

Ana danganta yawan hare-haren da ake kai wa kasar ta Kenya, da kungiyar tsageru ta al-Shaabab mai alaka da al-Qaeda da ke Somaliya, wadda ita da kanta sau da yawa ta kan fito fili da dauki alhakin hare-haren. Kasar ta Kenya ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen gabashin Afirka.

Mawallafi : Suleiman Babayo
Edita : Saleh Umar Saleh