Kokarin dakushe aikin kungiyar IS a Iraki | Labarai | DW | 16.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin dakushe aikin kungiyar IS a Iraki

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri da zai kai ga karya kashin bayan masu kishin addini a Iraki da ke fafutukar kafa daular musulunci.

Kwamitin dai ya ce zai sanya takunkumi da ma katse dukannin wasu kafofi da ke samar da kudi da makamai ga kungiyoyin masu kaifin kishin addini wadanda ke gudanar da aiyyukansu a kasar ta Iraki da kuma Siriya.

Burtaniya ce dai ta fara gabatar da wannan shawara gaban kwamitin wanda kuma aka amince da shi da gagarumin rinjiye. Da ta ke tsokaci kan wannan batu, mai baiwa shugaban Amirka shawara kan harkokin tsaro Susan Rice ta ce wannan kuduri da aka amince da shi cigaba ne sannan zai taimaka wajen hade kasar ta Iraki waje guda.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar