Kisan wani dan siyasa na bangaran milki a Burundi | Labarai | DW | 19.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan wani dan siyasa na bangaran milki a Burundi

Wasu mutane bakwai sanye da riguna masu surke dauke da bindigogi ukku suka iske mutuman a cikin wata mashaya tasa suka bude masa wuta.

A Kasar Burundi wasu mutane da ba a kai ga tantance ko su wa ne ba sun bindige shugaban jamiyyar CNND-FDD da ke mulki ta Shugaba Pierre N'kurunziza a cikin yankin Gitanga na kasar.Hukumar 'yan sanda ta kasar ce ta bada wannan labarin a yau juma'a .Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya wakana ne a daren Larabar da ta gabata inda wasu mutane bakwai sanye da riguna masu surke irin na sojoji da 'yan sanda dauke da bindigogi ukku suka iske mutuman a cikin wata mashaya tasa suka bude masa wuta.

Hukumar 'yan sandar kasar ta ce tuni ta soma gudanar da bincike domin gano makasan.Wani rahoto na wata kungiyar kare hakkin Dan Adam ta kasar ta Burundi ya bayana cewa kimanin mutane 70 suka halaka tun bayan barkewar rigingimun siyasar kasar da ke da nasaba da yinkurin Shugaba Pierre N'kurunziza na yin tazarce.