1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kisa a Tibet

April 23, 2011

An zargi 'yan sandan China da kashin wasu 'yan Tinbet biyu a cikin wani samame da suka kai a wurin ibada a garin Ngaba-abin da ɓata ran Dalai Lama shugaban addinin wannan yanki.

https://p.dw.com/p/1132n
Wani matashi ɗauke da tutar yankin TibetHoto: DW

Wata ƙungiyar Amirka mai fafutukar kare haƙkin al'umar yankin Tibet na ƙasar China ta ce 'yan sandan China sun kashe wasu mazauna ƙauyen Tibet su biyu a cikin wani farmaki da suka kai akan wani wurin ibada na addinin Budha. Ƙungiyar mai suna International Campaign for Tibet ta ce mutanen sun mutu ne bayan da aka yi musu dukar kawo wuƙa a ranar Ahamis a lokacin da suke ƙoƙarin hana 'yan sanda tsare ɗaruruwan limaman Budha daga wurin ibada Kirti da ke garin Ngaba. Tun ranar 11 ga watan Afrilu ne rikici ya ɓarke tsakanin dakarun tsaro da al'umar Tibet bayan da aka samu raɗi-raɗin cewa gwamnati ta yi shirin ɗaukar wasu limamai matasa domin ta sake basu horo. Gwamnatin yankin na Tibet da ke gudun hijira ta yi kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa da ta shawo hankalin China da kada ta yi amfani da ƙarfin tuwo akan mazauna wannan wuri. Shugaban addinin Tibet, Dalai Lama ya nuna matuƙar damuwarsa game da wannan al'amari.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal