1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Kirsimeti 2021: Paparoma na son a mutunta dan Adam

December 25, 2021

Kimanin mabiya 2000 tare da wasu malaman addini 200 ne suka saurari jawabin na Paparoma a a chocin St. Peter's Basilica a Vatican.

https://p.dw.com/p/44owS
Vatikan Christmette Papst Franziskus
Hoto: Filippo Monteforte/AFP

Shugaban mabiya darikar katolika ta duniya Paparoma Francis ya yi kira ga mabiyansa da su gode wa kalilan da Allah ya huwace musu a rayuwa. A jawabinsa na jajibirin Kirsimeti na bana, Paparoma ya ce Kirstocin da ke kuntata wa talaka na yin mummunan sabo.

Paparoman ya yi bayani a kan darajar dan Adam, inda ya ce Ubangiji yana tunasar da mabiya muhimmancin kula da hakkin ma'aikata maza da mata. Ya ce ya kamata a kawo karshen mutuwar da wasu ke yi a wuraren ayyukansu. 

Dokokin corona sun rage kusan sau biyar na adadin mutanen da ke halartar jawabin na shekara-shekara. Sai dai wadanda ba su zo wurin ba sun kalli jawabin kai tsaye ta hanyar bidiyo daga gidajensu.