Kira da babbar murya don kawo karshen rikicin Siriya | Labarai | DW | 21.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kira da babbar murya don kawo karshen rikicin Siriya

Kungiyoyi kusan 100 ciki har da kungiyar agaji ta Red Cross da Oxfam da wasu kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suka shiga cikin wannan yekuwa.

Manyan kungiyoyin agaji na duniya sun fara wani gagarumin shiri na kasa da kasa da nufin hada karfi da karfe don kawo karshen yakin kasar Siriya. Kusan kungiyoyi dari ne ciki har da kungiyar agaji ta Red Cross da Oxfam da World Vision da kuma wasu hukumomi da dama na Majalisar Dinkin Duniya suka shiga cikin wannan yekuwa da aka kaddamar a birnin Geneva. Kungiyoyin sun yi tuni da cewa a farkon shekarar 2013 da yawa daga cikin kasashen duniya sun yi kira da a kawo karshen mawuyacin halin da ake ciki a kasar ta Siriya mai fama da yakin basasa. Amma har yanzu ana ci gaba da zubar da jini sannan halin da ake ciki ya kara yin muni. A cikin kwanaki masu zuwa ne za a bude sabuwar tattaunawa kan neman zaman lafiya a Siriya.