Kiki kaka a game da sakamakon zabe a Italiya | Labarai | DW | 11.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiki kaka a game da sakamakon zabe a Italiya

Kasashen Faransa da Luxemburg sun mika sakon taya murna ga tsohon shugaban kungiyyar tarayyar turai, wato Romano Prodi bisa nasarar da jam´iyyar sa ta samu a zaben gama gari da aka gudanar a Italiya.

Kasashen biyu, sun tabbatar da cewa basu da shakkun wannan nasara zata bawa Romano Prodi dama na yin amfani da sanin makamar aiki daya samu, wajen kusanto da kasar cikin kungiyyar Eu.

Jam´iyyar dai ta masu sassaucin ra´ayi, da tsohon shugaban kungiyyar Eu kewa jagoranci, tace itace ta lashe zaben gama gari da aka gudanar a kasar, koda yake tuni jam´iyyar Faraminista ta Berlusconi tayui watsi da wannan furici.

Kafafen yada labaru dai sun rawaito cewa da alama cikakken sakamakon zaben zai kasance ne da kunnen doki a tsakanin jam´iyyun biyu.

To sai ya zuwa yanzu babu wani kalami a hukumance daga hukumar zaben kasar dangane da cikakken sakamakon zaben.