1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Khan ya yi alkawarin yakar rashawa a Pakistan

Zainab Mohammed Abubakar
August 18, 2018

A wannan Asabar din ce aka rantsar da fitaccen zakaran wasan Kirket na Pakistan Imran Khan a matsayin sabon fraministan kasar, wanda ya yi alkawarin yakar cin hanci.

https://p.dw.com/p/33Lbs
Pakistan - Imran Khan ist der neue Ministerpräsident
Hoto: picture-alliance/Photoshot

 A wani jawabi mai kakkausar murya da ya yi a gaban majalisar dokoki, Khan ya yi alkawarin bude sabon babi na hukunta masu almundahana da dukiyar kasa.

" Kama daga wadanda suka sace dukiyar kasa zuwa wadanda suka karbo rancen makuddan kudade, na yi wa Allah alkawarin cewar bazan bar kowannensu ba. Kuma wannan shi ne alkawarina ga al'ummar kasa. Zan dawar da dukkan kudaden Pakistan da aka sace aka boye a kasashen waje".

A jiya juma'a ce dai, Khan ya lashe kuri'un da 'yan majalisar Pakisatan din suka kada da gagarumin rinjaye, makonni uku bayan zaben kasa baki daya, wanda 'yan adawa suka yi zargin sa hannun jami'an soji da arangizon kuri'u.