1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenyatta: 'Yan sanda su bi a sannu

August 14, 2017

Shugaba Uhuru Kenyatta ya yi kira ga bangaren adawar kasar da ya kiyaye tunzura husuma kan zabe, yana mai shawartar 'yan sandan kasar da su bi a sannu.

https://p.dw.com/p/2iCFf
Kenia Unruhen nach dem Wahlenergebnis
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya yi kira ga bangaren adawar kasar da ya kiyaye tunzura husuma kan zabe, yana mai ba shi shwarin ya kai batun gaban kuliya. Wannan kiran na shugaba Kenyatta na zuwa ne yayin da wasu ruwayoyi ke cewa tuni jagoran adawa Mr. Raila Odinga ya fara nazarin kalubalantar sakamakon zaben, wanda ya bai wa shugaba Kenyatta nasara, bayan bijirewa yin hakan da ya yi tun farko. Shugaban na Kenya ya kuma yi kiran 'yan sandan kasar da su bi a sannu, a aikin da suke yi na murkushe tashin tashin tashin tashina da ke a kasar.

Dan takaran na hamayya mai shekaru 72, da fari dai ya shaida wa magoya bayansa da su kauracewa zuwa aiki a wannan Litinin don juyayin wadanda suka mutu sanadiyyar rigimar bayan sanar da sakamakon zaben da yammacin Juma'ar da ta gabata. Rahotanni na nunin cewa harkokin yau da kullum sun koma yadda aka saba a manya da kananan garuruwa na kasar.