1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya zata dauki likitoci aiki daga waje

Abdul-raheem Hassan
May 14, 2018

Ma'aikatan lafiya 1,000 ne gwamnatin ke shirin dauka aiki daga kasar Kuba, amma kungiyar likitoci na ganin ba a yi wa 'yan kasar adalci ba.

https://p.dw.com/p/2xhzG
Kenia nach der Annulierung der Präsidentenwahl | Uhuru Kenyatta
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

A shekara ta 2017 ne dai shugaba Uhuru Kenyata ya amince da kudurin, sai dai an fara cimma yarjejeniyar shirin ce a yayin ziyarar da ya kai Kuba a watan Maris da ta gabata.

Kungiyar likitocin kasar Kenya dai ta koka kan yadda gwamnati ke kokarin haramta wa 'yan kasar damar samun aiki, kungiyar ta ce akwai likitoci 2,000 da ke jiran a daukesu aiki.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce kowani likita daya a kasar Kenya na kula da marasa lafiya dubu 16,000 a maimakon likita daya ga majinyata 1000 kacal, sai dai gwamnatin ta zargi likitocin da rashin kwarewar aiki.