Kenya za ta ci gaba da kyale dakarunta a Somaliya | Labarai | DW | 01.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya za ta ci gaba da kyale dakarunta a Somaliya

Shugaban Kenya ya sha alwashin ci gaba da tallafa wa gwamnatin Somaliya wajen yaki da al-Shabab.

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya, ya bayyana cewar, kasar, za ta ci gaba da kyale dakarunta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya domin taimakawa gwamnatin kasar ta Somaliya wadda ke tangal-tangal ci gaba da tinkarar kungiyar al-Shabab, wadda ta kai hari a kan cibiyar kasuwanci ta birnin Nairobi a ranar 21 ga watan Satumban da ya gabata. Kungiyar ta ce harin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 67, martani ne ga dakarun da kasar ta Kenya ta tura a Somaliya da ke makwabtaka da kasar tun a shekara ta 20011. Hakanan kungiyar ta yi wa Kenya kashedin cewar, za ta ci gaba da fuskantar makamancin harin da ta kai a cibiyar kasuwancin - muddin dai ba ta janye dakarunta daga kasar ba. A lokacin wani taron addu'a a wannan Talatar (01. 01. 13), shugaba Kenyata ya ce zai samar da wata hukumar bincike, wadda za ta tantance wuraren da aka samu kuskure ta fuskar tsaro domin kiyaye gaba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu