1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan da ake wa ciki na Karuwa a Kenya

August 8, 2023

Wani kiyasi na Hukumar Kula da Yawan Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, na nunar da cewa kimanin yara 'yan mata dubu 330 a kasar Kenya ne ke samun juna biyu a duk shekara.

https://p.dw.com/p/4UvM4
Kenya I Kibera | Yara Mata
Koyar da yara mata yadda za su zabi dan takara a unguwar marasa galihu ta KiberaHoto: Donwilson Odhiambo/ZUMA/picture alliance

Wannan kiyasi na Hukumar Kula da Yawan Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniyar  ta fitar dai, na zaman adadin da ke sanya firgici. Sai dai duk da haka akwai 'yan matan da suka zama iyaye, wadan ke da burin samar da rayuwa mai inganci ga yaransu da ma su kansu kamar wasu 'yan mata biyu da ke da unguwar Kibera. Wadannan matasa biyu dai, sun kudiri aniyar yin watsi da duk wani nau'i na nuna kyama da wariya da al'umma ke musu, ko kuma abin da suke tsammani daga garesu ta hanyar komawa makaranta domin ci gaba da karatu. Esther Kamau ta samu juna biyu tana da shekaru 16 kacal a duniya, sai dai maimakon ta ajiye makaranta tana son ci gaba da karatunta da ma fatan sauya wa iyalanta muhalli. Ita kuwa Sharon Wanjiku mai shekaru 17 a duniya da ke da yaro dan shekaru uku da haihuwa, tana da burin zama malama da za ta shugabanci al'umma da kuma kare kananan yara mata.

Kenya | Nairobi | Kibera | Yara
Rayuwar kananan yara a unguwar marasa galihu ta Kibera da ke KenyaHoto: Getty Images/AFP/R. Schmidt

Cibiyar AIC Kibera, ta zama wani fata ga Wanjiku da Kamau da ma sauran 'yan matan da suka haihu. Da tallafin da take hadawa tsakanin mambobinta, wannan cibiya na taimakon 'yan matan da suka haihu su koma makaranta. Al'ummar yankin na kuma taimakon wadannan 'yan mata, wajen fita daga talauci. Ba wai karatu kawai ake koya musu ba, har ma da sana'o'in da za su dogara da kansu da ma yadda za su sarrafa kudi. Shugaban makrantar da ke koyar da su Charles Omwanza na da amannar cewa ilimi shi ne matakin farko na yakar talauci, sai dai ya nuna damuwa matuka kan yadda ake samun karuwar 'yan matan da ke haihuwa. Labarin Wanjiku da Kamau labarin biyu cikin 'yan matan Kibera ne kawai, wadanda suka rungumi fatan samun ilimi mai amfani. Duk da haka dai akwai bukatar ilimantarwa a Kenya ga maza da mata, domin rage samun 'yan mata da ke daukar juna biyu.