Kenya: Gobara ta hallaka dalibai 8 | Labarai | DW | 02.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kenya: Gobara ta hallaka dalibai 8

Hukumomi a Kenya sun ce a kalla 'yan mata 8 ne suka rasu yayin da wasu goma suka jikkata bayan da wata gobara ta tashi a dakin kwanan dalibai na wata makarantar kwana da ke Nairobi babban birnin kasar.

Ma'aikatar ilimin kasar ta ce tuni aka rufe makarantar kana aka fara bincike kan musababbin gobarar wadda ta tashi da misalin karfe biyu na daren jiya Juma'a. Guda daga cikin daliban makarantar da ke da yawan dalibai dubu dari 200 ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar wata daliba ce ta tashesu lokacin da wutar ta kama, wanda hakan ya taimaka wajen samun karancin asarar rai.