1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude rumfunan zaben Kenya

August 9, 2022

Tsadar rayuwar da kasar ke ciki a yanzu ka iya sanya jama'ar kasar mantawa da kabilanci a rumfar zabe, sabanin zabukan baya da kabilancin kan taimaka wa 'yan siyasa samun nasara.

https://p.dw.com/p/4FIX9
Kenia Wahlen 2022
Hoto: Patrick Meinhardt/AFP

An bude rumfunan zaben shugaban kasa a kasar Kenya a safiyar wannan Talata, inda madugun adawa Raila Odinga da ke samun goyon bayan shugaba mai barin gado ke fafatawa da mataimakin shugaban kasa William Ruto da ke tutiya da gwagwarmayarsa da ta kai shi har mukamin mataimakin shugaban kasa. 

Karfin mutanen biyu da karbuwarsu a siyasar Kenya ya sanya wasu ke tunanin watakila aje zagaye na biyu a karon farko a tarihin siyasar kasar da ke zama mafi karfin tattalin arziki a gabashin Afirka. Mutum sama da miliyan 22 ne ake sa ran za su kada kuri'a zaben.