Keken ruwa | Himma dai Matasa | DW | 26.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Keken ruwa

Yayin da ake ci gaba da samun ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na Najeriya, wani matashi a kasar da ke karatu a wata makarantar sakanderen kimiya a garin Funtuwa da ke Jihar Katsina ya kirkiro wani keken ruwa.

Wannan keken ruwa domin kubutar da jama'a da ka iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa, kusan a iya cewa wannan shi ne karan farko da aka kirkiri keken da zai iya tafiya cikin ruwa a Najeriya.

Shi dai wannan matashi Umar Bala da ya kirkiro wannan keken ruwa ya ce dama shi kullun kwakwalwarsa tana raya masa ya kirkiro wani abu na daban wanda ba a taba kirkira ba a Najeriya.

Kirkirar wannan keken ruwa dai ya ba wannan matashi Bala damar zuwa gasar baje kolin kere-keren fasaha na duniya a kasar Amirka inda kuma ya yi babbar nasasa. Tuni dai majalissar dokokin Jihar Katsina ta yi wata doka da za ta bai wa gwamnati jihar ta rika taimakon matasa masu fasa a jihar kamar yadda mataimakin kakakin majalissar dokokin jihar Shehu Dalhatu Tafoki ya tabbatar.