Kawar da ta′addanci a yammacin Afrika | Labarai | DW | 17.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kawar da ta'addanci a yammacin Afrika

Kasashen Burkina Faso da Mali sun amince su yi aiki tare da nufin kawar da aiyyukan ta'addancin na kungiyoyin da ke da kaifin kishin addini a yammacin Afirka.

Karkashin wannan matsaya da suka cimma bayan da firaministocin kasashen biyu suka yi wata ganawa dazu, kasashen biyu suka ce jami'an tsaronsu za su rika yin musayar bayanai na sirri tsakaninsu.

Har wa yau, Bamako da Ouagadougou sun amince su rika yin suntiri tare da nufin dakile dukannin wani yunkurin na kai hare-hare daga 'yan ta'adda.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da wata kungiya da ke da alaka da Al-Qaida ta kai hari Otal din Splendid da ke birnin Ouagadougou na Burkina Faso inda suka hallaka mutane da suka tasamma 30.