Kawancan masu mulki sun yi nasara a zaben Senegal | BATUTUWA | DW | 02.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Kawancan masu mulki sun yi nasara a zaben Senegal

Sakamakon farko na zaben 'yan majalisun dokokin kasar Senegal da ya gudanar a karshen mako, ya nunar cewa gamayyar jam'iyyun da ke mulki sun yi nasara a mafi yawan yankunan kasar.

Senegal Protest (dapd)

Masu zabe a kasar Senegal

Zaben 'yan majalisar dokoki zabe ne da tun farko ke a matsayin zakaran gwajin dafi na gwada farin jinin Shugaban kasar ta Senegal mai ci a yanzu wato Macky Sall a gaban babban abokin hamayyarsa Abdoullaye Wad da ke zama tsohon shugaban kasar mai shekaru 91 da kuma ke da niyyar kalubalantar shugaban kasar. Amma a zahiri ta ke cewa tsohon shugaban na da jan aiki a gabansa ta la'akari da irin kayen da jam'iyarsa ta PDS ta sha a zaben 'yan majalisar dokokin na wannan karo, inda kawancan  jam'iyyun da ke mulki ya lashe zaben a jihohi 43 daga cikin 45, hasalima jam'iyyar magajin garin birnin Dakar Khalifa Sall wanda ake tsare da shi yanzu haka a gidan kurkuku a bisa zargin cin hanci ne ya zo na biyu a yayin da jam'iyyar PDS din ta kare a matsayin ta uku. Moussa Diau, masanin kimiyyar siya a kasar ta Senegal, ya yi tsokaci kan wannan batu.

Macky Sall Präsident Senegal (Getty Images/AFP/T. Charlier)

Shugaban kasar Senegal, Macky Sall

"Lalle tsohon shugaban ya yi tashen farin jini, to amma kar ku manta da yadda al'umma ta juya masa baya a lokacin da ya so yin tazarce. kamata ya dau darasi domin matsalar jagoranci da ta taso a jam'iyyar sa, ta haddasa ficewar wasu jiga-jiganta da suka kafa nasu jam'iyyu ya rage karfin jam'iyayar."

Senegal Dakar Wahl (picture-alliance/abaca)

Yayin kada 'kuri'a a kasar senegal

Hukumar zaben kasar ba ta kai ga wallafa sakamakon zaben a hukumance ba. To amma tuni kawancan jam'iyyun da magajin garin birnin Dakar Khalifa Sall, ya musanta ikirarin lashe zaben birnin na Dakar da jam'iyya mai mulki ta yi, yana mai cewa shi ya lashe zaben ba tare da wata tababa ba kuma a shirye suke su kalubalanci kawancen masu mulki a gaban kuliya kan wanann batu. Wani zabi da Jam'iyyar PDS ta Abdoulaye Wade ta ke da shi dai, shi ne na tsayar da takarar Karim Wade dan tsohon shugaban a zaben shugaban kasa na 2019. To saidai Moussa Diau na ganin da wuya Karim wade din ya kai labari:

"Ba na tsammanin danshi zai iya kai labari, domin matsalar wadannan jam'iyyu , jam'iyyu ne na masu akidar bin mutun  kawai, kuma jagora daya ne , kuma shi ma dazaran ya kasance ya rike mulki kowa sai ya watse. Amma idan dan nashi na son shiga siyasa, yana iya dawowa Senegal ya yi gwagwarmaya kamar sauran shugabannin siyasa, ya gwada tashi sa'a. Amma ba na tsammahanin za a mika mushi mulkin gadon ubanshi. wannan zamani ya wuce  ba za ta yu a hakan ta kuma faru ba a Senegal."

Abdoulaye Wade (PA/dpa)

Tsohon shugaban kasar Senegal, Abdoulaye Wade

A tsakiyar mako ne ake sa ran hukumar zaben Senegal, za ta bayyana sakamakon zaben a hakumance, kafin daga karshe kotun tsarin mulkin kasar ta bayyana kammalallen sakamakon zaben sabuwar majalisar mai kunshe da kujeru 165 da suka hada da 15 na 'yan kasar mazauna kasashen ketare da kuma ke da wa'adin aiki na tsawon shekaru biyar.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin