Katar ta zargi hadaddiyar daular Larabawa | Labarai | DW | 17.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Katar ta zargi hadaddiyar daular Larabawa

Kasar Katar ta zargi hadaddiyar daular larabawa da tsara kutse da aka yi wa hanyoyin Intanet na kamfanin dillancin labarun kasar da ma wasu shafukanta na sada zumunta.

Kasar ta Katar dai ta ce hadaddiyar daular ta larabawa ta taka dokokin kasashen duniya kan 'yancin bayanai da wannan abin da ta yi.

Jaridar Washington Post ta kasar Amirka ce dai ta ruwaito wasu jami'an leken asirin Amirkar na tabbatar da hannun hadaddiyar daular ta larabawa a wannan rigimar kutsen.

Cikin watan Mayun da ya gabata ne kamfanin dillancin labaran kasar Katar ya wallafa wasu jerin sanarwa da aka danganta su da sarkin kasar, sanarwar da ta zamo sanadin rikicin diflomasiyya da kasar ke ciki da wasu 'yan uwanta na yankin Gulf.

Shi dai sarkin na Katar Tamim bin Hamad Al Thani, ya yaba karfin ikon kasar Iran ne, da ya ce da wuya a yi babu ita a yankin larabawa, kuma ba zai da ce a yake ta ba.

Sai dai hadaddiyar daular larabawan ta musanta zargin na kasar ta Katar.