Kataloniya ta kira yajin aikin gama gari | Labarai | DW | 02.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kataloniya ta kira yajin aikin gama gari

Kungiyoyin kwadago na yankin Kataloniyar sun yi kira zuwa ga wani yajin aiki na gama gari a gobe Talata domin nuna rashin amincewa da amfani da karfi wajen neman hana gudanar da zaben raba gardama.

Kungiyoyin kwadago na yanklin Kataloniyar kasar Spain sun yi kira zuwa ga wani yajin aiki na gama gari a duk fadin yankin a gobe Talata domin nuna rashin jin dadinsu dangane da yadda 'yan sanda suka yi amfani da karfin tuwo wajen hana gudanar da zaben rabagardama kan batun samun 'yancin kan yankin. 

A cikin wata sanadrwa da ta fitar a wannan Litinin Kungiyar Barcelona ta sanar da da cewa za ta shiga itama wannan yajin aiki inda tun daga rukunin manya na kungiyar har zuwa na makarantar horas da matasanta za su kauracewa filayen wasa a gobe Talatar. 

Dabra da wannan yajin aiki, majalisar dokokin Turai ta sanar da saka batun rikicin yankin na Kataloniya a jerin maudu'an da jadawalin taron da Kungiyar za ta gudanar a ranar Laraba mai zuwa a birnin Strasbourg.