Kataloniya: Masu son aware sun yi rinjaye | Labarai | DW | 02.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kataloniya: Masu son aware sun yi rinjaye

Shugaban yankin Kataloniya Carles Puigdemont ya bayyana cewa al'ummar yankin sun zabi ficewa daga kasar Spaniya.

Gwamnatin yankin Kataloniya ta bayyana gagarumar nasara ga wadanda suka zabi ta ware a kuri'ar raba gardama mai cike da cece-kuce da aka kada a ranar Lahadi inda kimanin mutane 800 suka samu raunika bayan taho mu gama da 'yan sanda lokacin da suka fita maci da kada kuri'a.

Shugaban yankin na Kataloniya Carles Puigdemont ya bayyana cewa al'ummar yankin sun zabi ficewa daga kasar Spaniya

"Kasar Spain ta yi rashi mafi girma na abin da ta rasa a baya al'ummar Kataloniya sun zabi zama masu cin gashin kansu."

Mai magana da yawun gwamnatin yanikin Jordi Turull ya fadawa manema labarai a wannan rana cewa fiye da kashi 90 cikin dari na mutane sama da miliyan biyu da dubu dari biyu sun ce a raba a kuri'ar raba gardamar da aka kada, kuri'ar da mahukuntan Madrid suka ce haramtacciya ce kuma 'yan sanda sunyi aikin da ya kamata, abin da su kuma 'yan fafuitika da 'yan kwadago suka bayyana da cin zarafi da ma kira na yajin aiki ranar uku ga watan nan na Oktoba.