Kataloniya cikin halin rashin tabbas | Labarai | DW | 11.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kataloniya cikin halin rashin tabbas

Shugaban gwamnatin kasar Spain Mariano Rojoy ya bai wa jagoran 'yan awaran Carles Puigdemont Kataloniya wa'adin kwanaki biyar domin ya ba da karin haske.

Tun farko Mariano Rojoy ya  gargadi shugaban 'yan awaran da cewar zai yi  amfani a karon farko da kudirin doka mai lamba 155 na kudin tsarin mulki  domin soke yancin kan na yankin idan har ya tabbatar. Daman a shekara ta 1934 gwamnatin ta Spain ta yi amfani da irin wannan doka wajen soke yunkurin wasu 'yan awaran  na kafa kasar ta  Kataloniya.