Kasuwar cinikin bayi a kasar Libiya | Labarai | DW | 11.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasuwar cinikin bayi a kasar Libiya

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta OIM ta bayyana takaicinta dangane da kasancewar wata kasuwa ta sayar da 'yan gudun hijira a matsayin bayi a yanzu haka a kasar Libiya. 

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta OIM ta bayyana takaicinta dangane da kasancewar wata kasuwa ta sayar da 'yan gudun hijira a matsayin bayi a yanzu haka a kasar Libiya. 

Babban jami'in hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta MDD a kasar Libiya Othman Belbeisi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Talata a birnin Geneva. Jami'in ya ce farashin dan gudun hijirar da ake sayarwa a matsayin bawa a kasuwar bayin ta Libiya na tashi daga dala 200 zuwa dala 500 ta Amirka.

Hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta ce wasu jami'anta da ke aiki a kasashen Libiya da Nijar sun samu cikakkun bayannan shaidu daga bakin wasu 'yan gudun hijirar kan yadda wasu 'yan kasar ta libiya tare da hadin bakin wasu 'yan Ghana da 'yan Najeriya suke sayar da daruruwan mutane maza da mata da sunan bayi a bainar jama'a, a kasuwannin cinikin bayi na musamman da aka kafa a kasar ta Libiya.