Kasashen duniya sun amince da tallafa wa Libya | Labarai | DW | 02.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen duniya sun amince da tallafa wa Libya

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya ce idan aka zauna ba a samu fahimtar juna ba cikin hanzari kungiyar IS na iya dagula lamura a kasar.

Schweiz UN-Sonderbeauftragte für Liyben Bernardino Leon in Genf

Bernardino Leon me shiga tsakani a rikicin Libya daga Majalisar Dinkin Duniya

Kasashen duniya karkashin Majalisar Dinkin Duniya a ranar Juma'ar nan sun bayyana bukatar samun hadin kai a tsakanin bangarori masu gaba da juna a Libya, inda suka nemi su bada goyon baya ga shirin zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniyar ke shiga tsakani in da su kuma a nasu bangaren suka bayyana aniyar tallafa wa wajen ganin an sake gina kasar, da kuma yin gargadin cewa ba zasu zauna ba suna ci gaba da ganin tashin hankali da ke faruwa a kasar.

Bayan watanni na samun tsaiko ga shirin sulhun na Majalisar Dinkin Duniya mai shiga tsakani daga majalisar Bernardino Leon ya mika takarda kunshe da bayanan shirin zaman lafiya da aka cimma na ranar 21 ga watan Satimba, abin da ke da burin ganin bayan cece-kuce da ke tsakanin bangarori biyu masu ikirarin mulkin kasar inda kowane bangare ke da wadanda ke dauke da makamai na mara masa baya.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry a wani bangare na taron koli na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa babu wani lokaci da za a zauna ana batawa ganin yadda mayakan IS ke kara samun gindin zama a kasar ta Libya.