Kasashen Duniya na ganawa a Amirka | Labarai | DW | 19.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Duniya na ganawa a Amirka

Ana sa ran shuwagabannin kasashen duniya za su tabka mahawara a zauren Majalisar Dinkin Duniya kan rashin tsaro a Siriya da batun tattalin arziki.

A taron dai ana sa ran cewar Babban sakataren MDD Ban Ki Moon wanda zai ajiye mukaminsa a ranar 31 ga watan Disamba da shugaba Barack Obama na Amirka da ke kammala wa'adin mulkinsa a watan Janairu, za su yi jawabinsu na karshe a gaban majalisar a yayin da firaministan Birtaniya Theresa May za ta yi fitowarta ta farko tun bayan dare kujera mulki a kasa da watanni uku da suka gabata bayan ficewar kasarta daga Kungiyar tarayyar Turai EU.