Kasashen Balkan sun takaita shigar ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Balkan sun takaita shigar 'yan gudun hijira

Sabiya da Masadoniya sun dauki matakin haramta wa 'yan gudun hijirar da suka fito daga kasashen da ba a yaki izinin ketarawa zuwa sauran kasashen Turai.

Kasashen yankin Balkan din dai sun dauki matakin tatar 'yan gudun hijirar da ke bi ta kasashensu domin shiga sauran kasashen Turai. Matakin ya tanadi haramta wa 'yan gudun hijirar da suka fito daga kasashen da ba sa fama da yaki izinin ketarar zuwa sauran kasashen Turan.

Kakakin Babban komishinan Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Melita Sunjic , ya ce tun a yammacin jiya Laraba hukumomin kasar Sabiyar suka takaice izinin shiga kasar tasu ga 'yan gudun hijirar kasashen Afganistan da Siriya da Iraki kawai.

Ita mai dai daga nata bangare kasar Masadoniya ta dauki matakin tatar 'yan gudun hijirar da suka fito daga kasar Girka inda ta haramta wucewa ga 'yan asalin kasashen Maroko da Sri lanka da Sudan ,Laberiya ,Kwango da kuma Pakistan.

Yanzu haka dai wannan mataki ya haifar da cinkoson 'yan gudun hijirar a bakin iyakokin kasashen biyu inda 'yan gudun hijirar sama da dubu biyu suka taru a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP