Kasashen Amirka da Iran na zama kan nukiliyar Iran | Labarai | DW | 16.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen Amirka da Iran na zama kan nukiliyar Iran

Manyan jami'an Amirka da Iran na ganawa a kasar Swizalan kan batun makamashin nukiliyar Iran.

Tattaunawa kan batun makamashin nukiliyar Iran, ta shiga wani muhimmin gaba a wannan Litinin, kasancewar Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry zai gana da takwaransa na Iran Mohammad Zarrif a birnin Lausanne na kasar Switzerland, domin cimma matsaya ta kwarai dangane da batun da a yanzu aka dauki watanni 18 ana tattaunawa kansa.

Yayin da lokaci ke kara matsowa, ana sa ran manyan jami'an kasashen biyu za su tattauna abin kirki a zaman da suke yi a Switzerland, wanda bayansa ne ake fatan kammala komi ranar 1 ga watan Yulin bana.

John Kerry Amirka tare da Mohammad Zarrif na Iran din dai, na fuskantar matsi daga wasu al'umomi a cikin gida, wadanda ke ganin akwai bukatar tsayuwar kasashen kan batun na nukiliya.

Tun farko dai Mista Kerry ya fada a kasar Masar gabanin kama hanyarsa ta zuwa Switzerland din, cewar burinsu dai shi ne cimma matsaya, matsaya kuwa ta hakika.