Kasashe daga EU sun taka matsayar tsaro | Labarai | DW | 13.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe daga EU sun taka matsayar tsaro

Kasashe 23 mambobi na Kungiyar Tarayyar Turai sun aza wani ginshiki na samar da tsaro (PESCO) ta hanyar aiwatar da yarjejeniyoyi da aka kulla ta fiskar tsaro da hadin kan sojoji na kasashen.

Ministocin harkokin wajen kasashen 23 da ministocin tsaronsu sun rattaba hannu a wannan rana ta Litinin kan wata matsaya da ke da buri ta samar da wani ginshiki na din-din-din don hada kai mai suna (PESCO), abin da zai sanya kasashen su samu hadin kai fiye da lokutan baya kan harkokin da suka shafi hadin kai na sojoji da ma yadda suke gudanar da aiyukansu.

A cewar shugabar tsare-tsare a harkokin kasashen waje a kungiyar ta EU Federica Mogherini, wannan matsaya da aka cimma ta kafa tarihi kan batun tsaro na Kasashen Turai. A cewar ministar harkokin tsaron Jamus Ursula von der Leyen wannan yunkuri zai sanya kasashen na Turai su tsaya da kafarsu ta fiskar tsaro musamman tun bayan zabin Shugaba Donald Trump na Amirka.