1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hargizi bayan zaben Zimbabwe

August 4, 2018

Zabubbukan da aka gudanar a kasashen Mali da Zimbabuwe su dauki hankalin jaridun na Jamus a wannan mako musamman amfani da karfi kan masu bore a Harare.

https://p.dw.com/p/32ci0
Mali Präsidentschaftswahl 2018 | Wahlplakate Keïta & Cissé
Hoto: DW/K. Gänsler

Mun fara sharhin jaridun ne da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi sharhi tana mai cewa sojoji sun share titunan birnin Harare, sai ta ci gaba tana mai cewa.

Shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa ya ba da sanarwa gudanar da bincike bayan tashin hankalibn da ya faru a ranar Laraba, inda dakarun tsaro suka bindige har lahira wasu magoya bayan jam'iyyar adawa ta MDC da ke bore don adawa da jinkiri wajen sanar da sakamakon zaben ranar Litinin. Wannan sanarwa ta Shugaba Mnangagwa ta zo gababin sanar da sakamakon zaben da hukumar zaben Zimbabuwen ta yi a daren Alhamis, inda ta ayyana jam'iyyar ZANU-PF mai jan ragamar mulki a matsayin wadda ta yi nasara a zaben. Tuni dai dan takarar adawa na jam'iyyar MDC Nelson Chamisa ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotu. 

Ita ma jaridar Berliner Zeitung ta yi sharhi mai taken "harbe-harbe a birnin Harare bayan fara bayyana sakamakon zabe".

Hargitsi duk da cewa ba Mugabe ne a kan mulki ba, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai cewa a Zimbabuwe jam'iyyar ZANU-PF ta tsohon shugaban kasa Robert Mugabe da aka tilasta masa yin murabus a bara, za ta ci gaba da mulki a kasar, sai dai 'yan adawa sun yi zargin an tabka magudi a zaben kasar da ya gudana a ranar Litinin, lamarin da ya haddasa mummunan tashin hankali har da rasa rayuka.

Simbabwe Wahlen  Ausschreitungen Gewalt
Hoto: Reuters/S. Sibeko

A can kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka an gudanar da zabe wanda bisa ga dukkan alamu za a je zagaye na biyu domin babu dan takara da ya samu yawan kuri'un da zai ba shi damar darewa a  kan karagar mulki.
A kan zaben na Mali jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi inda ta fara da cewa zabe a cikin yanayi na ta'addanci. Ta ce a ranar Lahadi aka gudanar da zaben shugaban kasa a Mali, amma a lokaci guda hare-haren ta'addanci sun dabaibaye wasu yankuna na kasar duk da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aka girke a kasar. Wannan ya sa ba a gudanar da zabe a wasu yankuna na arewacin kasar ba. Amma duk da haka zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana. Saboda fargabar ka da a zubar da jini an girke dakarun tsaro kimanin dubu 30. A lokutan baya bayan nan dai al'amuran taro sun tabarbare a kasar ta Mali.

Hawaye da hayaki mai sa hawaye lokacin da Bemba ya koma gida, wannan shi ne taken rahoton da jaridar Die Tageszeitung ta rubuta dangane da komawar Jean-Pierre Bemba gida a tsakiyar mako.
Ta ce bayan da kotun duniya mai hukunta manyan laifun yaki da ke birnin The Hague na kasar Holland ta wanke shi, Bemba da ke zama jaogran adawa a Kwango kuma tsohon jagoran 'yan tawaye, ya koma kasarsa jamhuriyar Demukaradiyyar Kwango inda ya samu gagarumar tarba daga magoya bayansa. Yanzu haka dai ana iya cewa komawarsa ta bude kamfen na yakin neman zaben shugaban kasar, inda zai fafata da shugaba mai ci Joseph Kabila.