Kasar Libiya ta fara farfadowa | Labarai | DW | 20.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Libiya ta fara farfadowa

Libiya ta fara fitar da man fetur zuwa kasashen ketere bayan rikicin ya shafe watanni da dama yana dagula lamuran siyasa da na tattalin kasar.

Kasar Libiya ta fara fitar da man fetur daga babbar tashar jiragen ruwan kasar, wadda aka rufe tun karshen shekarar da ta gabata, lamarin da zai karfafa matsayin gwamnatin kasar da ke neman kawo karshen rikici tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai. Tashe-tashen hankula da aka samu mafi yawa a filayen jiragen saman biranen Tripoli da Benghazi sun tabarbara lamura tare da janyo janyewar jakadun kasashen duniya masu yawa daga kasar.

A wannan Laraba Ministan kula da harkokin man fetur na kasar na wucin gadi Omar Shakmak ya mika takardar neman ajiye aiki kamar yadda Firaminista Abdullah al-Thinni ya bukata, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito. Kasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka mai arzikin man fetur na kungiyar OPEC ta fada rudanin siyasa tun shekara ta 2011 bayan juyin-juya halin da ya kawo karshen gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi ta fiye da shekaru 40.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe