Kasar Jordan ta soma mayar da martani ga IS | Labarai | DW | 04.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Jordan ta soma mayar da martani ga IS

Bayan kisan da 'yan kungiyar IS suka yi wa matukin jirgin saman yakin Jordan Maaz Al-Kassasbeh, hukumomin kasar sun aiwatar da kisa kan wasu 'yan Jihadi guda biyu.

Da sanyin safiyar wannan Larabar ce dai hukumomin na Jordan suka aiwatar da wannan kisa ga mutanen biyu cikinsu har da matar nan 'yar Jihadi ta kasar Iraki mai suna Sajida Al-Rishawi da 'yan kungiyar ta IS suka nemi a sako ta kafin su bada bailin matukin jirgin saman na Jordan. Da farko dai 'yan kungiyar ta IS sun sanar cewa ba za su kashe matukin jirgin Maaz Al-Kassasbeh dan kasar ta Jordan ba, muddin dai hukumomin kasar suka sallamo musu wannan mata. Hukumomin na Jordan sun nuna fushinsu sosai, inda suka ce kashe wannan matashin sojan zai kara karfafa hadin kan 'yan kasar wajen yakar 'yan ta'adda.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal