Kasar Hungary na adawa da rabon ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 03.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Hungary na adawa da rabon 'yan gudun hijira

Kotun kolin kasar Hungary ta amince da bukatar gwamnati ta shirya zaben raba gardama kan tsarin kungiyar Tarayyar Turai na rarraba 'yan gudun hijira.

Ungarn PK Orban zur Flüchtlingskrise

Firaministan Hongri Viktor Orban

Tun farko dai wanda Firaministan kasar Viktor Orban ya nuna adawarsa kan wannan batu na rarraba 'yan gudun hijira ga kasashe membobin kungiyar EU. Wasu kanana jam'iyyun adawa ne suka shigar da wannan batu a gaban kotun kolin kasar, inda ita kuma ta amince da tsarin da gwamnatin kasar ta yi.

A tsakanin watan Agusta mai zuwa ne dai da Disamba, gwamnatin kasar ta Hungry ke fatan shirya wannan zaben na raba gardama kuma tun a watan Afrilu ta soma yakin neman zabe na nuna kin amincewarta da wannan bukara ta Tarayyar Turai.