1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Guinea ta rabu da annobar Ebola

Mouhamadou Awal Balarabe
June 19, 2021

Watanni biyar bayan sake bullar Ebola a Guinea Conakry, gwamnatin kasar da Hukumar Lafiya ta Duniya sun bayyana kawo karshen zagaye na biyu na annobar, wacce ta kashe m mutanen 12 a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/3vDMq
Afrika Ebola in Guinea (Symbolbild)
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Palitza

Hukumar Lafiya ta Duniya da gwamnatin Guinea Conakry sun sanar da kawo karshen zagaye na biyu na annobar Ebola , 'yan watanni kalilan bayan sake bullarta a wannan kasa ta yammacin nahiyar Afirka.  Ministan lafiya na Guinea Rémy Lamah da wani jami'in WHO, Alfred Ki-Zerbo ne suka yi shelar ayyana karshen Ebola a Guinea, a lokacin wani bikin hadin gwiwa a garin Nzérékoré inda cutar ta sake bayyana a karshen watan Janairu.

Akalla mutane 23 ne dai suka kamu da cutar ta Ebolar, wacce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, a cewar bayanin da WHO ta fitar a ranar Asabar.  Hukumomin na Guinea da na duniya sun yi saurin shawo kan annobar ta Ebola idan aka kwatanta da wacce aka yi fama da ita tsakanin 2013 zuwa 2016, inda ta yadu zuwa kasashen Laberiya da Saliyo. 

A wancan lokaci dai, sama da  mutane 11,300 suka kamu da Ebola, galibinsu a Guinea da Laberiya da Saliyo, da suka kasance a rukunin kasashe mafi talauci a duniya.