Kasar Gini ta kawar da cutar Ebola | Labarai | DW | 29.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Gini ta kawar da cutar Ebola

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta sanar da kawo karshen annobar cutar Ebola a kasar Guinea makonnin shida bayan warkar da mutun na karshe da ya kamu da cutar

A wannan Talata ce Hukumar lafiya ta Duniya wato WHO ko OMS ta bayyana a hakumance kawo karshen annobar cutar Ebola kwata-kwata daga kasar Guinea makonnin shida bayan warakar mutun na karshe da ya kamu da cutar a kasar.

Kasar Guinea ta kwashe shekaru biyu tana fama da annobar cutar ta Ebola wace ta halaka mutane dubu biyu da 536 daga cikin dubu uku da 804 da suka kamu da cutar.

Tun a ranar 16 ga wannan wata na Nowamba ne dai aka bayyana warakar Noubia wata jaririya da mahaifiyarta ta haifata da cutar a cibiyar kula da masu dauke da cutar Ebola ta birnin Konakry.