Kasar Burundi na cikin rudani | Labarai | DW | 13.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasar Burundi na cikin rudani

Bangarorin da ke rikici da juna a kasar Burundi sun amince da shiga zauren tattaunawa kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bukata.

halin da ake ciki a Burundi

halin da ake ciki a Burundi

Ko da yake har yanzu majalisar ta ce ba ta samu gamsasshiyar amsa daga bangaren gwamnatin ba. Rahotanni sun nunar da cewa bangaren gwamnati da na 'yan adawa sun yi maraba da kiran na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya bukaci da su gaggauta zama kan teburin sulhu domin kawo karshen rikicin siyasar kasar da ke kokarin rikidewa zuwa yakin basasa kana ake fargabar ka iya juyewa zuwa kisan kiyashi. Hakan dai ya sanya Majalisar Dinkin Duniyar tunanin tura dakarun wanzar da zaman lafiya domin kare afkuwar kisan kiyashin. Sai dai a hannu guda wani fitaccen dan adawa a kasar ta Burundi ya yi kira ga majalisar da ta tura dakarun wanzar da zaman lafiyar nata zuwa kasar ganin yadda al'amura ke kara rincabewa.