1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar mutuwar bakin haure a teku

Ahmed SalisuAugust 15, 2015

Kimanin mutane 40 aka ba da labarin rasuwarsu cikin wani jirgin ruwa da ke makare da bakin haure da ke kokarin tsallakawa zuwa Turai daga gabar ruwan Libiya.

https://p.dw.com/p/1GFzW
Flüchtlinge erreichen Hafen von Palermo
Hoto: picture alliance/ZUMA Press/A. Melita

Mai magana da yawun sojin ruwan Italiya Costantino Fantasia ne ya shaida hakan inda ya ce suna kyautata zaton rashin iska ce ta hallaka su yayin da suke makale a cikin wajen ajiyar kaya na jirgi.

Kamfanin dillancin labaran Italiya na ANSA ya ce yanzu haka masu aikin ceto na Italiya na kokarin ceto mutane 300 da jirgin ke dauke da su kuma ma tuni suka samu nasarar ceto wasu da ke da sauran shan ruwa a gaba.

Wannan na zuwa ne bayan da a ranar Talatar da ta gabata wasu mutane kimanin 50 suka rasu sanadiyyar nutsewar da jirginsu ya yi a tekun Bahar Rum.