Karshen gaba tsakanin Kiir da Machar | Labarai | DW | 22.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Karshen gaba tsakanin Kiir da Machar

Bangarorin dake gaba da juna a Sudan ta Kudu wato na shugaban kasa salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar sun sasanta tsakaninsu.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta kuma 'yan tawayen kasar sun cimma yarjejeniyar hadin kai, bayan da suka shafe watanni 13 suna kai ruwa rana tsakaninsu.Tattaunawar da ta gudana a Arusha da ke arewacin Tanzaniya, ta bayar da damar dinke barakar da ke tsakanin bangarorin SPLM dake gaba da juna.

Rikicin da ya barke tsakanin shugaba Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar a kashen shekara ta 2013 ya haddasa mutuwar mutane sama da dubu biyu yayin da akalla mutane miliyan daya suka kaurace a matsugunansu.